GODIYA TA MUSAMMAN GA MASARAUTAR GUSAU A KAN AMINCEWA DA BADA SARAUTAR JARUMIN GUSAU GA ANAS HAMISU ANALYS!
Daga; Nura Muhammad Mai Apples Gusau
------------------------------¥-----------------------------
Hakika muna mika godiyar mu Ga Allah Madaukakin Sarki Mai kowa mai Komai Wanda Cikin ikonsa ya Nufa Anka Baiwa Mai Gidanmu Sarautar (JARUMIN GUSAU) Gaskiya babu ko Kokontu wannan Sarautar ta dace da shi, kuma ta cencenceshi, kasancewarsa Mutum mai Biyayya haziki kuma gwazo.
Hon, Anas Hamisu Analyst Jarumin Gusau. muna matukar murna da alfahari da wannan Sarautar ta JARUMIN GUSAU da anka baiwa Wannan bawan Allah,
Anas Hamisu Analyst JARUMIN GUSAU ya kasance abin ko'i ga Al'umma Wajan bada gudun muwa ta kowane fanni domin ci gaban al'ummar Gusau da kewayenta, yunkurinsa wajan bada tallafi ga matasa da kyakkyawar manufofinsa na Alkhairi.
Mai Alfarma Sarkin katsinan Gusau Dr. Ibrahim Bello Sardaunan konaka, muna Addu'ar Allah ya dafa maka ga duk kanin al'amurranka kuma ya baka nasara akan mulkin ka ya daukaka Masarautar Gusau da masu son ci gabanta,
A gefe daya kuwa, muna amfani da wannan damar wajan taya babban mai gidanmu murnar bashi wannan Sarautar kuma Allah ya dafa maka ya sanya Albarka kuma ya Baka damar kara kaini wajan tallafawa al'ummah.
Muna Addu'ar Allah ya baka Gusau ta daya cikin sauki,
Daga Nura Muhammad Mai Apples Gusau
Comments
Post a Comment