Skip to main content

Posts

Korar Malamai 21,780: Gwamna El-Rufai Yayi Amai-Ya-Lashe

​ A cewar sa gwamnatin ta jihar za dai ta maida hankali ne wajen sake horar da malaman dake iya samun horo sannan kuma ta canzawa wadanda ba su iya samun horo wuraren ayyuka na daban domin samun sahihin sakamako daga wajen su. Majiyar mu dai ta samu a baya ne dai gwamnatin ta gudanar da wata jarabawar tantancewa ta ‘yan ajin Furamare 4 ga malaman na su inda aka samu cewa akalla malamai 21,780 ne suka fadi jarabawai bayan da sakamako ya fita. Bayan daa hakan ta auku ne kuma ma dai sai gwamnatin ta sha alwashin korar dukkan wadanda suka kasa cin wannan jarabawar sannan kuma suka bayyana aniyar su ta sake daukar sabbin ma’aikata 25,000 don maye gurbin su.

Dakarun Hadin Kan Afirka Zasu Fatattaki Mayakan Al-Shabab Daga Somalia

Dakarun Hadin Kan Afirka Zasu Fatattaki Mayakan Al-Shabab Daga Somalia ​ Dakarun hadin kan Afirka, AU, a Somalia Dakarun kungiyar tarayyar Afirka ta AU sun kaddamar da wani shiri a kasar Somalia da zai fatattaki mayakan kungiyar al-Shabab daga yankin Shabelle, a kuma killace hanyar shigar da kayayyaki zuwa yankin. Shaidu sun fadawa sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, sun ga sojojin kungiyar AU akan hanya da kuma wani yanki da ake noma tsakanin garin Afgoye da Bal’ad, sun kuma lura da cewa babu ‘yan kungiyar al-Shabab dayawa a yankin jiya Litinin. Aikin da kungiyar tarayyar Afirka ke yi a Somaliya, da ake kira AMISOM, a wata sanarwa an fadi cewa an kaddamar da shi ne bayan da aka samu bayanai kan cewa kungiyar Al-Shabab na kawo rashin kwanciyar hankali a babbar hanyar da ta hada Mogadishu da filin saukar jiragen sama na Ballidogle, mai tazarar kilomita 90 arewa da babban birnin tarayya. Ballidogle dai filin jiragen saman sojoji ne dake yankin Shabelle, inda dakaru...

PDP Ta Zargi Gwamnatin Katsina Da Gaza Tabuka Abin Kirki

PDP Ta Zargi Gwamnatin Katsina Da Gaza Tabuka Abin Kirki ​ Jam`iyyar PDP mai adawa a Najeriya da kuma a Katsina ta yi zargin cewa tun lokacin da takwararta APC ta kwace mulkin jihar daga hannunta babu wani abin kirkin da ta tsinana wa jihar tsawon kimanin shekara uku. Shugaban PDP a jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya ce ayyukan raya kasa sun tsaya cik, hatta wasu manyan ayyuka da gwamnatinsu ta fara aiwatarwa, amma ba ta kammala gabanin ta bar mulki ba, duk an yi watsi da su. Ya ce ayyukan sun hadar da Kasuwar Dubai da kwalejin fasahar sadarwa, ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar ta fi mayar da hankali wajen runton aiki ta hanyar yi wa makarantun da gwamnatinsu ta gina fenti. Haka zalika, PDP ta zargi jam’iyyar APC da karbo bashin biliyoyin naira ba tare da aiwatar da aikin a-zo-a-gani ba. Sai dai APC ta musanta wadannan batutuwa, ta ce PDP ba ta da bakin magana idan aka yi la`akari da dumbin bashi da mawuyacin halin da ta bar al`ummar jihar a ciki. Shi ...

Shugaba Buhari Ya Shirya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2018.

Shugaba Buhari Ya Shirya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2018. ​ Yau Talata ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin badi, a gaban majalisar dokokin Najeriya, kuma shine karo na uku da gwamnatin zata gabatar cikin kasafin kudi daya ta’allaka akan nema domin babu adanannun kudi. Kasafin kudin Najeriya na wannan karon ka iya shan bam-ban da na sauran shekarun da suka gabata, dalili kuwa shine gangar man fetur ta haura zuwa kusan dala sittin. A watannin da suka gabata, shugaba Muhammadu Buhari, ya yi ta kokawa musamman akan yadda tsagerun Niger-Delta ke fasa bututun mai, koda shike wannan matsala ta kare duk da barazanar da ‘yan tsageran Avengers suka yi ta dawo da kai hare-hare. Ko mai talakawa ke cewa dangane da kasafin kudin kasar, Mukhtar Sodangi Binanci, talaka ne mai lura da lamurran yau da kullum a Najeriya, ya bayyana cewa wasu dai-daiku ne kadai ke karuwa da manya manyan ayyukan da gwamnati take gudanarwa a Najeriya, domin har yanzu a cewars...

Shugaba Trump Ya Sami Bayanan Sirri Kan Rikicin Nukiliyar Da Koriya Ta Arewa.

Shugaba Trump Ya Sami Bayanan Sirri Kan Rikicin Nukiliyar Da Koriya Ta Arewa. ​ Shugaba Trump Da Uwargidansa Melania, da furannin Hawa’ii da aka karrama su da su. Ranar Jumma’a shugaban ya sauka a Hawa’ii inda daga nan ne zai tashi zuwa Asiya. A dai dai lokacinda zaman dar dar ta karu a makuridn koriya, rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Pacific a jiya jumma’a, ya gabatar wa shugaban Amurka Donald Trump bayanan sirri. Rundunar ta gabatar da wannan bayanan ne da saukar jirgin shugaban na Amurka da ake kira “Air Force One” da turanci, a tsibirin Oahu, ind a shi da uwargidansa Melania Trump suka sami tarbo ta gargajiyar Hawa’II inda aka saka musu makawiyar furanni da ake kira Leis. Daga nan shugaba Trump ya wuce kai tsaye zuwa cibiyar rundunar sojojin kundunbalar Amurka mai kula da yankin Pacific, runduna mafi girma wacce ta hada duka sassan mayakan Amurka. “Kuna da jarumai da dakaru masu basira, kuma muna farin ciki da godiya,” shugaba Trump ya gayawa Admiral Harry ...

Doyin Okupe Ya Kalubalanci Buhari A Kan Fita Da Alex Ekwueme Kasar Waje Don Yin Magani

Doyin Okupe Ya Kalubalanci Buhari A Kan Fita Da Alex Ekwueme Kasar Waje Don Yin Magani ​ Doyin Okupe, tsohon mataimakin na musamman a kan harkokin hulda da jama’a ga tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya zargi gwamnatin Buhari game da shirin fita da tsohon mataimakin shugaban kasa, Dokta Alex Ekwueme zuwa kasar waje don yin magani. majiyar mu. ta ruwaito cewa Ekwueme wanda yanzu haka yana mai shekaru 85, a cikin makon nan ya fadi, sannan aka kai shi asibiti a shiyar Neurosurgery a Trans-Ekulu da ke jihar Enugu. Okupe, memba na Jam’iyyar Accord, ya bayyana shawarar fita da Ekwueme kasar waje a matsayin “abin da bai kamata ba, inda ya jaddada cewa “akwai iyaka ga farfaganda.” Kamar yadda Okupe ya rubuta a shafinsa ta Twitter cewa: “Sanarwar da aka bayar game da yadda za a fita da Cif Ekwueme kasar waje ba daidai ba ne. Hakazalika, kwamitin kare ‘yancin dan Adam (CDHR) ta kalubalan ci wannan yunkurin

Shugaba Buhari Zai Kewaye Jihohin Kudu Maso Gabashin Najeriya

Shugaba Buhari Zai Kewaye Jihohin Kudu Maso Gabashin Najeriya ​ Gwamnan jihar Imo Rochas Okoracha ya bayyana a ranar da ta gabata cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai je yawon rangadi a cikin jihohin Kudu Maso gabashin kasar nan domin inganta dangartakar sa da Inyamurai. A cewar gwamnan, ya ziyarci shugaban kasa a fadar sa dake birnin tarayyar domin kara dankon zumunta a zukatan al’ummar kudu maso gabashin kasar nan. majiyar mu ta fahimci cewa, gwamna Okorocha shine kadai gwamnan da aka zaba na jam’iyyar APC a yankin da kuma shi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu mafi karancin kuri’a a zaben 2015 da ya gabata. Okorocha ya bayyana cewa, “akwai bukatuwar shugaban kasa ta yayi azamar zuwa yankin Kudu Maso gabashin kasar nan a daidai wannan lokaci, kuma an yi sa’ar shugaban kasa zai ziyarci jihar Ebonyi sannan ya garzaya jihar Imo kafin ya karasa jihar Anambra”. Gwamnan ya kuma bayyana hangen nesan sa na cewar, jam’iyyar APC z ta cigaba da samun mambobin sakamakon ‘...