Skip to main content

PDP Ta Zargi Gwamnatin Katsina Da Gaza Tabuka Abin Kirki

PDP Ta Zargi Gwamnatin Katsina Da Gaza Tabuka Abin Kirki







Jam`iyyar PDP mai adawa a Najeriya da kuma a Katsina ta yi zargin cewa tun lokacin da takwararta APC ta kwace mulkin jihar daga hannunta babu wani abin kirkin da ta tsinana wa jihar tsawon kimanin shekara uku.

Shugaban PDP a jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya ce ayyukan raya kasa sun tsaya cik, hatta wasu manyan ayyuka da gwamnatinsu ta fara aiwatarwa, amma ba ta kammala gabanin ta bar mulki ba, duk an yi watsi da su.

Ya ce ayyukan sun hadar da Kasuwar Dubai da kwalejin fasahar sadarwa, ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar ta fi mayar da hankali wajen runton aiki ta hanyar yi wa makarantun da gwamnatinsu ta gina fenti.

Haka zalika, PDP ta zargi jam’iyyar APC da karbo bashin biliyoyin naira ba tare da aiwatar da aikin a-zo-a-gani ba.

Sai dai APC ta musanta wadannan batutuwa, ta ce PDP ba ta da bakin magana idan aka yi la`akari da dumbin bashi da mawuyacin halin da ta bar al`ummar jihar a ciki.

Shi dai Majigiri na cewa: “Maganar ilmi da noma da kula da lafiya dukkansu ba bangaren da ya ci gaba, sai baya da muka mika mulki. Kuma mun bar kudi sun kai biliyan 14 a asusun gwamnati, sannan zuwa yanzu ta karbi sama da biliyan 300 amma a nuna min aikin wani aiki na miliyan 500 da za a iya budewa a jihar Katsina.”

Ya ce makarantun da gwamnatinsu ta bari ne, jam’iyyar APC take bi tana yi musu fenti maimakon fentin Najeriya da suke da shi. A cewarsa: Da ya ji ruwan damuna zai wanke, fenti aiki ne?”

Shugaban jam`iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Shitu Shuaibu Shitu ya ce hasali ma, kura-kura da PDP ta tafka ne suka jefa Katsina a halin da ta samu kanta, don haka bai kamata ta zake tana hakikicewa ba.

Ya ce zamanin mulkin PDP, gwamnatinsu ba ta dauki hakkin ma`aikata a bakin komai ba, duk kuwa da irin gudummuwar da suke bayarwa wajen raya kasa da ciyar da jihar gaba.

Jam`iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana mulkin jihar Katsina. Sai a 2015 ne ta sha kaye a hannun jam`iyyar APC.

Manufar caccaka da sukar da abokan adawar siyasa kan yi dai, kamar yadda masana ke cewa, ita ce ankarar da jam`iyya mai mulki don ta gyara tafiyarta.

Amma a Najeriya ba kasafai jami`yya mai mulki ke kallon lamarin a matsayin gyara kayanka ba, sakamakon zargin cewa ba da kyakkyawar niyya aboakan hamayya kan yi hakan ba.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020