A cewar sa gwamnatin ta jihar za dai ta maida hankali ne wajen sake horar da malaman dake iya samun horo sannan kuma ta canzawa wadanda ba su iya samun horo wuraren ayyuka na daban domin samun sahihin sakamako daga wajen su.
Majiyar mu dai ta samu a baya ne dai gwamnatin ta gudanar da wata jarabawar tantancewa ta ‘yan ajin Furamare 4 ga malaman na su inda aka samu cewa akalla malamai 21,780 ne suka fadi jarabawai bayan da sakamako ya fita.
Bayan daa hakan ta auku ne kuma ma dai sai gwamnatin ta sha alwashin korar dukkan wadanda suka kasa cin wannan jarabawar sannan kuma suka bayyana aniyar su ta sake daukar sabbin ma’aikata 25,000 don maye gurbin su.
Comments
Post a Comment