Shugaba Buhari Zai Kewaye Jihohin Kudu Maso Gabashin Najeriya
Gwamnan jihar Imo Rochas Okoracha ya bayyana a ranar da ta gabata cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai je yawon rangadi a cikin jihohin Kudu Maso gabashin kasar nan domin inganta dangartakar sa da Inyamurai.
A cewar gwamnan, ya ziyarci shugaban kasa a fadar sa dake birnin tarayyar domin kara dankon zumunta a zukatan al’ummar kudu maso gabashin kasar nan.
majiyar mu ta fahimci cewa, gwamna Okorocha shine kadai gwamnan da aka zaba na jam’iyyar APC a yankin da kuma shi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu mafi karancin kuri’a a zaben 2015 da ya gabata.
Okorocha ya bayyana cewa, “akwai bukatuwar shugaban kasa ta yayi azamar zuwa yankin Kudu Maso gabashin kasar nan a daidai wannan lokaci, kuma an yi sa’ar shugaban kasa zai ziyarci jihar Ebonyi sannan ya garzaya jihar Imo kafin ya karasa jihar Anambra”.
Gwamnan ya kuma bayyana hangen nesan sa na cewar, jam’iyyar APC z ta cigaba da samun mambobin sakamakon ‘yan siyasa da dama dake ta shiga jam’iyyar a halin yanzu.
A cewar gwamnan jihar Imo, babu tantama a cancantar shugaba Buhari na sake neman kujerar zabe a karo na biyu a zaben 2019 mai gabatowa, sai dai tilasa ne ya biyo tafarkin zabe a mataki na farko don kaucewa takkadamar sauran ‘yan takarar.

Comments
Post a Comment