Skip to main content

KUNGIYAR STUDENT ALLIANCE SUPPORT OF BELLO MUHAMMAD MATAWALLE (SA-BELMAT)

KUNGIYAR STUDENT

tayi zama yau daya daga cikin wadanda suka kirkiro da wannan kungiya wato Comrade Umar Mahmud Umar, ya ce; "babban makasudin zaman shine munga ya dace mu fito a matsayinmu na 'yan jiha, kuma a matsayinmu na wani yanki daga cikin daliban jihar Zamfara muyi godiya ta musamman bisa ga irin gwaggwarmaya da chanji da Hon Luqman Majidadi ya kawo karkashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Zamfara na bashi wannan jagorancin, da kuma shi gwamna a bisa babban aikin da ya dauko wajan ganin a samu ilimi a cikin jihar Zamfara".

Ya ce; "kamar yadda muka sani akwai dalibai wajan 700 daga jihar zamfara wadanda aka dauko kuma aka tantance mutum 200 daga ciki zasu je suyi karatun a bangare daban-daban tun daga abinda ya shafi bangare tiyata da kuma hada magunguna da sauransu, wanda insha Allahu nan da shekaru zuwa goma zamu samu 'yan asalin  jihar Zamafar da suka samu kwarewar da zasu ci gaba da kula da 'yan uwansu a cikin kauyuka da kuma biranen jihar Zamfara, wanda in aka dubi tun inda aka fito shekara goma ba'a taba samun gwamnatin da tazo cikin lokaci daya ta daukin nauyin dalibai sama da 200 ba, ko kuma wani abu mai kama da haka, sai a karkashin jagorancin wannan gwamna, to shi yasa muka ga ya kamata muzo mu bayyanawa duniya jin dadinmu a bisa irin wannan namijin kokari da ake yi".

Yace; "kamar yadda kuke gani irin namijin kokarin da shugaban daliban jihar Zamfara wato (Hon, Kuqman majidadi keyi, tun daga wajan tantance dalibai, hadi da samar masu da tikiti da kula dasu da samar masu da muhali  mai kyau a  kasashen ketare  abun yabawa ne". Yace; zuwan Majidadin, ke da wuya a ofis ya dukufa wajan ziyarce-ziyarce a wasu manyan jami'o'in kasar nan, domin yin bincike akan shin wane bashi ne waccan tsohuwar gwamnati ta bari wanda su yanzu zasu dubi kokarin da ya kamata suyi, saboda akwai daliban jihar Zamfara masu karatu Al'hikima har yanzu basu karbi dakardunsu ba, akwai wasu an kaisu sunyi karatu a kasar India biyan kudin ya gagara, to wannan ba karamin kokarin bane" a cewar Comrade Umar.

Haka ya kara da cewar "kungiyar (Sa-Belmat) tun lokacin da aka kirkireta ta samar da ayyukanyi ga matasa". A karshe yayi godiya ga gwamna Bello Muhammad Matawalle akan rakiyar da yayi wajan ganin cewa an wayar da kan jama'a kan cin hanci da rashawa. Haka yayi addu'ar samun zaman lafiya da arziki mai albarka a jihar Zamfara da Najeriya baki daya.

Sharhi;

munyi jinjina sosai da wannan kungiya idan maka dubi irin kokarinta wajan samar da cigaba ga matasa, muna fatan gwamnatin gwamna Bello Muhammad Matawalle zata kara kaini domin ganin matasan jihar Zamfara sun samu ilimi mai nagarta wanda zai taimaki jihar nan ta kowane bangare

Daga Nura Muhamad Mai Apple Gusau

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!

A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...