Skip to main content

Posts

SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA KANSILAN GUNDUMAR GALADIMA, GUSAU (HON. UMAR KWACCIDO) NE GWARZON KANSILA, NA ZAMFARA!

SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA KANSILAN GUNDUMAR GALADIMA, GUSAU (HON. UMAR KWACCIDO) NE GWARZON KANSILA, NA ZAMFARA! Kamar yadda Kungiyar MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA ta shirya zaben jin ra'ayin jama'a akan Wanda ya dace ya zama GWARZON KANSILA a tsakanin takwarorinsa na Jahar Zamfara. Hon. Umar Kwacchido, Gusau. Bayan ya zama zababben KANSILA a mazabar Galadima dake Gusau, an shede shi da kyakkyawan hali da riko da addinin isalama da ma son talakkawan da ya ke cikinsu. Domin karrama shi tare da kara masa karfin guiwar cigaba da yiwa al'ummarsa ayukkan azo a gani. Wanda Hakan zai kara karfafa takwarorinsa, wajen kula da Al'umma. la'akkari da wadannan hujjoji kamar haka da al'umma sunka fada akan wannan KANSILA; 1- BANGAREN YAKI DA FATARA. * Ya sayawa matasa Babura suna kabu-kabu har 42 a yankin Galadima, inda mutun za su biya shi, kudin duk sati Dubu biyar har su mallake shi. * Haka zalika ya baiwa ...

'Barin malamai su rike bindiga zai magance matsalar harbe-harbe'

Trump ya ce barin malamai su rike bindiga zai kawo karshen matsalar harbe-harbe Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a ganinsa abun da ka iya kawo karshen matsalar yawan harbe-harbe a makarantu a Amurka, shi ne horar da malamai su iya amfani da bindigogi. Ya bayyana hakan ne a wani taro da ba a taba yin irinsa ba a Amurka, inda wadanda su ka tsira a harbe-harben da a ka sha yi a makarantu da iyayen wadanda su ka mutu su ka gana da Shugaban ido da ido. Taron wani yunkuri ne na jawo hankalin shugabannin siyasa su sauya ra’ayi a kan manufofin amfani da bindiga a kasar. A taron da a ka watsa a gidajen talabijin, daya daga cikin mahaifan wadanda su ka mutu a wani harbi da a ka yi a wata makaranta, ya nuna bacin ransa ga kalaman Mr Trump. Inda ya bayyana su a matsayin masu tsananin rauni.

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kudirin samar wa makiyaya filayen kiwo a jihohi

Gwamnatin tarayya ta ba kowace jiha damar daukan matakin da zai kawo karshen rikicin makiyaya a kasar Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kudirin samar wa makiyaya filayen kiwo a jihohi Kwamitin mutane 10 da majalissar zartarwa ta kafa dan kawo karshen hare-haren makiyaya wasu sassan kasar, ta ba kowace jiha damar daukan matakin da take ganin zai kawo karshen matsalar. Kwamitin wanda mataimakin shugaban kasa, Ferfesa Yemi Osinbanjo yake jagoranta, ya hadda da gwamnonin jihar Zamfara, Kaduna, Adamawa, Benuwe, Filato, Ebonyi da Oyo. Wani babban jami’in fadar shugaban kasa ya fadawa manema labaru a ranar Lahadi cewa, gwamnatin tarayya bata son ta tilasatawa jihohi yin abubuwan da basa son yi. Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kudirin samar wa makiyaya filayen kiwo a jihohi Yace mataikamakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana haka wani taro da suka yi. Jami’in wanda baya son a bayyana sunan shi yace, mataimakin shugaban kasa ya lura da irin fargaban da wasu jihohi suk...

Buhari ya rattaba hannu a kan dokar ƙara wa ‘yan majalisu ƙarfin iko a kasar nan

Buhari ya rattaba hannu a kan dokar ƙara wa ‘yan majalisu ƙarfin iko a kasar nan A ranar Juma’ar da ta gabata ne, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan wata sabuwar doka ta ƙara wa ‘yan majalisu ƙarfin iko a kasar nan. Wannan doka ta baiwa ‘yan majalisun tarayya da kuma na jihohi wata dama ta kare su daga duk wani laifukan furuci da suka aikata, inda ta kuma faɗaɗa ikonsu na umartar jami’ai wajen cafke duk wani da ya saɓawa dokokin su. Shugaban kasa; Muhammadu Buhari majiyar Mai Apple, ta kuma fahimci cewa, dokar ta bayar da iko ga ‘yan majalisu na kiranyen duk wani mutum ya gurfana a gaban su domin bayar da wata shaida akan kowane bincike da suke gudanarwa. Jaridar Daily Trust ta ruwaito da sanadin hadimin shugaban ƙasa akan harkokin majalisun tarayya, Sanata Ita Enang, inda ya bayyana cewa shugaban ya kuma rattaba hannu a kan wasu sabbin dokoki bakwai da ‘yan majalisun su ka buƙata. A ranar da ta gabata ne kuma, Majiyar Mai Apple, ta ruwaito cewa, shugaba ...

Gwamnan Kaduna zai kori masu gadi da ‘yan sako marasa takardun Makaranta daga aiki

Kawo yanzu haka Gwamnatin Jihar Kaduna na cigaba da sallamar Ma’aikatan Jihar da dama. A baya dai Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya sallami Malaman Makaranta rututu har 21,780 da kuma Ma’aikatan kananan Hukumomin Jihar. Yanzu kuma dai Gwamnatin Jihar ta Kaduna ta shirya korar masu gadi da ‘yan sako watau masinjoji daga aiki. Gwamnan ya bada umarni cewa ayi waje da duk Ma’aikacin da ya zarce fiye da shekaru 10 yana aiki bai da takarda akalla difloma. Gwamna El-Rufai dai yana ta kokarin kawo gyara a harkar aikin Gwamnati inda yake sassabe Ma’aikata. Kwanakin baya ma dai ya shiga Hukumomi da Makarantun Gwamnatin Jihar ban da kuma Ma’aikatan Masarautu da ya kora a baya. Idan ba ku manta ba kwanan nan wani Dattijo da aka sallama da ke aikin Masinja a Sabon-Gari Zaria ya fadi war-was. A da dai an yi tunani ya rasu amma majiyar mu ta bayyana mana cewa doguwar suma ce kurum tsohon Ma’aikacin yayi.

Hukumar raya birnin Abuja za ta rushe wasu gine-gine 750

Hukumar raya birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce za ta rushe a kalla wasu gine-gine kimanin 750 a unguwar Lugbe domin kiyaye mazauna wurin fadawa cikin hatsari. Darekta a hukumar, Mista Mukhtar Usman Galadima, ya sanar da haka yayin ziyarar yankin gine-ginen da abin zai shafa, yana mai bayyana cewar dukkan gine-ginen basu samu sahalewar hukumar ba kafin a gina su. Galadima ya bayyana cewar anyi gine-ginen ne a karkashin babban layin wutar lantarki, kuma za’a rushe su domin bawa kamfanin raba hasken wutar lantarki sararin yin aiki da kuma kiyaye afkuwar hatsari. ” Nisan da hukuma ta yarda da shi tsakanin kowanne irin gini da babban layin wutar lantarki shine mita 30 ,” a cewar Galadima. Gine-gine dake Unguwannin Tudunwada da Peace Village ne rusau din zai fi shafa. Ko a kwanakin baya saida ministan aiyuka, gidaje, da lantarki, Babatunde Raji Fashola, ya ce gwamnatin tarayya za ta rushe duk wasu gine-gine da aka yi a karkashin babban layin wutar lantarki da kuma wadanda aka yi...

Za a sauya mattatun da Shugaban Kasa ya ba mukami kwanaki

Yanzu haka dai mun ji cewa Fadar Shugaban Kasa za ta sauya mattatun da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba mukami a Gwamnatin sa kwanaki wanda hakan ya jawo abin maganar ira_iransu. Mai magana da bakin Shugaban Kasar watau Mal. Garba Shehu ya tabbatar da cewa za sake yi wa mukaman da aka bada kwanaki wani kallo inda za a cire sunayen wadanda su ka rasu a maye gurbin su da wasu dabam kwanan nan. Garba Shehu yace za kuma a cire sunayen wadanda yanzu haka sun bar Jam’iyyar APC amma an sa sunan su a mukaman da aka bada kwanaki. Garba Shehu ya bayyanawa Jaridar Punch wannan ne a wayar tarho da su kayi. Daga cikin wadanda aka ba mukaman akwai wasu da su ka rasu tuni, wasu kuma dai sun bar APC zuwa wasu Jam’iyyun adawar. A cikin wadanda Gwamnatin Tarayya ta ba mukaman har da na kusa da Atiku Abubakar da ya koma PDP.