Skip to main content

SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA KANSILAN GUNDUMAR GALADIMA, GUSAU (HON. UMAR KWACCIDO) NE GWARZON KANSILA, NA ZAMFARA!

SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA KANSILAN GUNDUMAR GALADIMA, GUSAU (HON. UMAR KWACCIDO) NE GWARZON KANSILA, NA ZAMFARA!



Kamar yadda Kungiyar MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA ta shirya zaben jin ra'ayin jama'a akan Wanda ya dace ya zama GWARZON KANSILA a tsakanin takwarorinsa na Jahar Zamfara.

Hon. Umar Kwacchido, Gusau. Bayan ya zama zababben KANSILA a mazabar Galadima dake Gusau, an shede shi da kyakkyawan hali da riko da addinin isalama da ma son talakkawan da ya ke cikinsu.

Domin karrama shi tare da kara masa karfin guiwar cigaba da yiwa al'ummarsa ayukkan azo a gani. Wanda Hakan zai kara karfafa takwarorinsa, wajen kula da Al'umma.

la'akkari da wadannan hujjoji kamar haka da al'umma sunka fada akan wannan KANSILA;

1- BANGAREN YAKI DA FATARA.

* Ya sayawa matasa Babura suna kabu-kabu har 42 a yankin Galadima, inda mutun za su biya shi, kudin duk sati Dubu biyar har su mallake shi.

* Haka zalika ya baiwa 'yan Kasuwa talatin (30) kowane Dubu hamsin-hamsin bashi a yankinsa, duk Wata su biya Dubu biyar.

BANGAREN ADDINI

* Ya gina masallaci a shiyar tudun faila.
Tare da bayar da gudummuwa zuwa ga masallatan hamsussulawat. Da tabarmi da sauransu.

* Ya Shirya Musabakar al'kur'ani a matakin yankinsa na Galadima

BANGAREN NEMAN ILIMI

* Ya dunka kaya da sanya yara makarantar Firamare  har mutun 600.

*Ya dunka kaya da sanya yara makarantar Sikandare su  har mutun 200

* Yakan taimakawa ya yan Makaranta domin zana Jarabawar kammala Sikandare.

* Ya kai matasa 15 a  makarantun gaba da Sikandare 5 a zacas 5  maru 5 Tsafe

* Shirya musabaka ta yan makarantun islamiya dake mazabarsa.

*Ya Gina Toilet a makarantar primary ta Malam wakkala dake hayin Mlm Ibrahim mai Tafseer.

*Yana kokarin samawa Matasan da ke kokarin wuce makarantar gaba da Sikandare takardar shedar zama 'yan yanki (indigent)

*Yana sayawa matasa masu kokarin shiga aikin kaki form a duk lokacin da Hakan ta tusgo.

BANGAREN AYUKKA DA YA YINA MUSAMMAN.

*  Taimakawa wajen gyara wata gada dake daura da nasiha kyamis dake mazabarsa, duk dacewa aikin na karamar hukuma ne. kwalbatin shiga kurmi da ta lalace, kwalbatin Dan durumi, Daura da Gidan Alh. Tukur Muhammad, kofar Jange, gyaran kwalbati a kofar Gidan Mamanu Sabon Fege

* Ya raba  Babura companion 6 a yankisa.

* Ya bada tallafi ga wanda bala'in ruwan sama ya sama a damanar bana na cement 200 da bulo 1000.

ya gina fanfonda ke bada ruwa fiyeda shekara bakwai har yanzu ana anfana dashi (wato kusada gidan marigayi Bala na Mada sabon fegi).

la'akkari da wadannan kwakkwaran dalillai da kyakkyawan ayukkan, Kungiyar MURYAR TALAKA ta yi Dogaro. Har ta aminta da cewa shi ne ya fi dukkannin takwarorinsa Kansiloli a Jahar Zamfara, Dan Haka zata baiwa wannan Dan tahalikin Lambar YABO a Babban taron Kungiyar da za ta yi a watan 3-2018 a Matsayin Kwarzon KANSILA a Jahar Zamfara.

Muna Taya shi murna, Allah ya ba shi ikon cigaba da yiwa Al'ummarsa abubuwan kirki, muna rokon Allah ya sa wannan kyautar ta kara masa azama. Daga karshe muna rokon Allah ya ba shi Wata kujera da ta fi wannan a 2019 domin cigaba da yiwa Al'umma hidima.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA. Da Nura Muhammad Mai Apple Gusau,  A madadin dukkanin shuwagabannin Kungiyar da membobinmu.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020