Hukumar raya birnin Abuja za ta rushe wasu gine-gine 750
Hukumar raya birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce za ta rushe a kalla wasu gine-gine kimanin 750 a unguwar Lugbe domin kiyaye mazauna wurin fadawa cikin hatsari.
Darekta a hukumar, Mista Mukhtar Usman Galadima, ya sanar da haka yayin ziyarar yankin gine-ginen da abin zai shafa, yana mai bayyana cewar dukkan gine-ginen basu samu sahalewar hukumar ba kafin a gina su.
Galadima ya bayyana cewar anyi gine-ginen ne a karkashin babban layin wutar lantarki, kuma za’a rushe su domin bawa kamfanin raba hasken wutar lantarki sararin yin aiki da kuma kiyaye afkuwar hatsari.
” Nisan da hukuma ta yarda da shi tsakanin kowanne irin gini da babban layin wutar lantarki shine mita 30 ,” a cewar Galadima.
Gine-gine dake Unguwannin Tudunwada da Peace Village ne rusau din zai fi shafa.
Ko a kwanakin baya saida ministan aiyuka, gidaje, da lantarki, Babatunde Raji Fashola, ya ce gwamnatin tarayya za ta rushe duk wasu gine-gine da aka yi a karkashin babban layin wutar lantarki da kuma wadanda aka yi ba bisa ka’ida ba a gefen hanyoyin gwamnatin tarayya.
Daga; Comrade Nura Muhammad Mai Apple Gusau, Dan kishin kasa
Comments
Post a Comment