Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kudirin samar wa makiyaya filayen kiwo a jihohi



Gwamnatin tarayya ta ba kowace jiha damar daukan matakin da zai kawo karshen rikicin makiyaya a kasar

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kudirin samar wa makiyaya filayen kiwo a jihohi
Kwamitin mutane 10 da majalissar

zartarwa ta kafa dan kawo karshen hare-haren makiyaya wasu sassan kasar, ta ba kowace jiha damar daukan matakin da take ganin zai kawo karshen matsalar.

Kwamitin wanda mataimakin shugaban kasa, Ferfesa Yemi Osinbanjo yake jagoranta, ya hadda da gwamnonin jihar Zamfara, Kaduna, Adamawa, Benuwe, Filato, Ebonyi da Oyo.

Wani babban jami’in fadar shugaban kasa ya fadawa manema labaru a ranar Lahadi cewa, gwamnatin tarayya bata son ta tilasatawa jihohi yin abubuwan da basa son yi.

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kudirin samar wa makiyaya filayen kiwo a jihohi
Yace mataikamakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana haka wani taro da suka yi.



Jami’in wanda baya son a bayyana sunan shi yace, mataimakin shugaban kasa ya lura da irin fargaban da wasu jihohi suka shiga akan kudirin gwamnatin tarrayya na ware makiyaya filayen kiwo.

Yace kwamitin ta yanke shawaran hada gwiwa da gwamnatin wajen karfafa hukumomin sharia da jami’an tsaro
Kwamitin ta na son a kara karafafa jami’an tsaro ta inda za su kama wandanda suke kashe-kashe da masu daukan nauyin su a fadin kasar.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’