Za a sauya mattatun da Shugaban Kasa ya ba mukami kwanaki
Yanzu haka dai mun ji cewa Fadar Shugaban Kasa za ta sauya mattatun da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba mukami a Gwamnatin sa kwanaki wanda hakan ya jawo abin maganar ira_iransu.
Mai magana da bakin Shugaban Kasar watau Mal. Garba Shehu ya tabbatar da cewa za sake yi wa mukaman da aka bada kwanaki wani kallo inda za a cire sunayen wadanda su ka rasu a maye gurbin su da wasu dabam kwanan nan.
Garba Shehu yace za kuma a cire sunayen wadanda yanzu haka sun bar Jam’iyyar APC amma an sa sunan su a mukaman da aka bada kwanaki. Garba Shehu ya bayyanawa Jaridar Punch wannan ne a wayar tarho da su kayi.
Daga cikin wadanda aka ba mukaman akwai wasu da su ka rasu tuni, wasu kuma dai sun bar APC zuwa wasu Jam’iyyun adawar. A cikin wadanda Gwamnatin Tarayya ta ba mukaman har da na kusa da Atiku Abubakar da ya koma PDP.
Comments
Post a Comment