Cikar Shekara Daya; Gwamna Matawalle a Sikelin Nazari!
Assalamu alaikum, Ranka ya dade barka da warhaka da fatan ana ci gaba da gudanar da mulkin wannan jiha cikin koshin lafiya. Allah ya sa haka. Ranka ya dade Sir, cike da girmamawa nake ta ya ka murnar cikarka shekara daya a kan karagar jagorancin al'ummar jihar Zamfara, ko shakka babu wannan babban abun farin ciki ne da sambarka. Allah ya maka jagora har zuwan wa'adin mulkinka. Ranka ya dade Sir! A nazarce kwanaki 360 da ka share kana jan ragamar jihar nan, ko shakka babu an samu cigaba a wurare da dama, kuma abun Yabawa ne a bisa wannan. Mu mun san cewa; ko da Allah madaukakin sarki ya baka jagorancin wannan jihar ka sameta ne a hargitse, cikin wani mummunan yanayi marar dadi, musamman ta fuskar tsaro, wanda a lokacin mutumin jihar Zamfara a kullum cikin fargaba yake sakamakon mummunan ta'adin 'yan ta'adda, wadanda suka yi sanadiyar rasa rayukan dubban mutune, hadi da cilastawa dubban mutane barin muhallansu ba cikin shiri ba. Hakika abun sambarka ne, ...