Makomar Najeriya a kasashen duniya a taron koli na majalisar dinkin duniya
KO NAJERIYA TA TABA SAMUN WANI ALFANU A CIKIN TARON DA TAKE HALLARTA A ZAUREN MAJALISAR DINKIN DUNIYA? Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya Kamar yadda ake ci gaba da gudanar da ire-iren wadannan tarurruka a shekara-shekara wanda wannan shine 74 a cikin jerin tattaunawar da ake a zauren majalisar dinkin duniya. Najariya Kasa ce Mai albarka kuma tana da kima da daraja a idon duniya Wanda hakan ya sa itama tana daya daga cikin manyan baki masu jawabi a cikin zauren na majalisar. Taron Wanda yake gudana, kuma manufar taron na bana shine kalubale na sauyin yanayi, Wanda ake kokarin ganin an tallafawa kasashen duniya masu fama da wannan matsalar, kuma a cikin taron har wasu gwamnatocin kasashen duniya sun Fara bayar da tallafinsu a cikin wannan shirin, shirin Wanda ya samu bakuntar kasashe 66 a bana. Shugaban majalisar dinkin duniya Antonio kutaresh Manyan kasashen da ...