Manufar Almajiri a Kasar Hausa
Abin da ake nufi da ALMAJIRI a kalmar Hausa, sunan ya samo asali ne a kasar Hausa tin lokacin da addinin musulunci ya fara samun karbuwa a kasar Hausa, har iyaye suka fara amincewa da bada 'ya'yansu karantarwa a makarantun Tsangayoyin Malaman da suka shigo da ilimin addinin Muslinci a kasar Hausa. Wanda sukayi imani a wancan lokacin, suka watsar da Bautar Aljani Giji a kasar Hausa, sai suke daukar kyautar Tufafi da Abinci Suna baiwa Almajirai saboda neman tsira da amincin Allah. Kafin zuwan karantarwar addinin musulunci karkashin tsarin (tsangaya) a kasar Hausa, Ana Bautar Aljannu ne, wadanda ake kira da suna(Giji) a kalmar Hausa, kusan kowane gida akwai (Giji), kuma kowace zuri'ah suna da (Giji), duk wata Masarautar da suka kafu a wancen lokacin suna da Babban (Giji) wanda duk Shekara al'ummar Garin suke Bauta masa duk Gari, idan ana neman Biyan Bukata ana Rokon (Giji) domin a samu biyan Bukata a lokacin jahiliyya. Daga cikin masu wayo a kasar Hausa tuni sun...