Wajibi ne muyi bincike kan mutuwar Mohammad Mursi - Majalisar dinkin duniya



Shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya bada kariya ga kiran da majalisar tayi na gudanar da bincike mai zaman kanta kan mutuwar tsohon shugaban kasar Misra, Mohammed Mursi.


Mataimakin mai magana da yawun shugaban MDD, Haq Farhan, ya bayyanawa kamfanin dillancin Najeriya NAN a birnin New York cewa Antonio Guterres na tare da duk abinda majalisar dinkin duniya ta fadi.



Farhan wanda ya bada amsa kan tambayar cewa shin me majalisar dinkin duniya za ta ce game da martanin kasar Misra cewa ana kokarin siyasantar da mutuwar Mursi.




Muhammad Mursi, shine zababben shugaban kasar Misra na farko a tarihin kasar, ya rasu ranar Litinin a kotu bayan shekara 6 da yi masa juyin mulki da jefashi gidan yari.

A ranar Talata, kwamishanan majalisar dinkin duniya kan kare hakkin dan Adam, ya yi kira ga bincike mai zurfi kan mutuwar Mursi.

A jawabinsa, mai magan da yawunsa, Rupert Colville, ya ce binciken ya game dukkan abubuwan da suka faru da Mursi cikin shekaru shida da aka tsareshi.


Yace: "Ya kamata a gudanar da bincike mai zaman kanta kuma wacce ba tada alaka da kasar da ta tsareshi. Wajibi ne a gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru da suka sabbaba mutuwarsa."



Ma'aikatar harkokin wajen Misra ta mayar da martani kan wannan jawabin cewa majalisar dinkin duniya na kokarin sanya baki cikin harkokin kasar da kuma batwa bangaren shari'arta suna.

Mun samu wannan labarin daga kamfanin Liget.com



ko shakka babu wannan babban labari ne Mai cike da faranta rai, muna fatan zai tabbata kuma a bi masa kadin sa.

Muna bada hakuri kasancewar mun yi amfani da hoton shugaba kasar Turkiyya ne ,ba na Majalisar dinkin duniya ba

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’