YA KAMATA A KOMA A HUTA ZAIFI DOMIN BAIWA WASU DAMAR MAYE GURBINKA!
Tun 1999 ake damawa da Kai a siyasar jihar nan, tun kafin zamanka a kujerar gwamna har ya kasance ka zama gwamna Mai cikakken iko a duk fadin jihar ta Zamfara, bayan kwashe shekaru Hudu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada, kuma ka nuna bukatar sake komawa kujerar jagorancin jihar a 2003 kuma ka samu damar zama gwamna a wa'adi na biyu ka ci gaba da jan ragamar jagorancin jihar har zuwa karshen zangon da aka tanadarwa kujerar gwamna a Najeriya.
Bayan nan ka tsinduma cikin neman kujerar Sanata a yankinka da ke Zamfara ta yamma a shekara ta 2007, bayan saukarka a kujerar gwamna a wancen lokacin, kuma Allah cikin ikonSa ka samu damar zuwa majalisar dattawa a shekara 2007 din, ka share shekaru Hudu cur ! mu dai babu wani abun kirki da mukaji ko muka gani kayiwa yankin naka, domin jindadi hadi da walwalar Al'ummarka.
Bayan nan ka dawo neman mukamin zama Sanata a wa'adi na biyu, kuma ka samu nasarar komawa a zauran majalisar dattawan a shekara 2011 a haka ka share shekaru Hudu babu komai wanda Al'ummar da Kake wakilta zasu bugi girjin cewa sun samu daga wajenka, kasancewar ka samu dukkanin goyon baya daga talakawan jihar baki daya Wanda kuma hakan ya samo asali ne tun lokacin da kana gwamnan jihar ta Zamfara, saboda yunkurinka wajen dabbak'a Shari'ar musulunci, Wanda Ta sanadiyar haka Zamfarar ta zama abun duba da k'ima a cikin jihojin Najeriya hadi da wasu kasashe masu sha'awar addinin musulunci.
Sannan bayan kaiwa karshen wa'adinka na 2015 ka Kara neman komawa kujerar jagorancin yankinka daga 2015 zuwa 2019 kuma ka samu cikakkiyar nasarar hakan, sanin kowane dan jihar Zamfara ne a matsayinka na shugaban limamin chanji a jihar Zamfara, kana da kowace irin dama wadda zaka iya amfani da ita domin gabatar da Kira "Motion" a Majalisa domin sanin halin da yankinka yake ciki na rashin tsaro domin samun dauki da agajin gaggawa, Amma kayi biris! Ka Kasa cewa uffan! a kan irin abinda yake faruwa a yankin naka Wanda kuma ya sabawa abinda aka tura ka dominsa.
Duk da haka a cikin wannan zango na 2019 kayi iya kokarinka domin ganin ka marawa Wanda talakawan jihar basu so baya, Amma cikin iyawar Allah hakan bai samu ba, yanzu kuma gashi kwatsam sai muka ganka a cikin gidan gwamnati, ko shakka babu kanmu ya dauran matuka inda muka cigaba da dasa ayar tambaya wa junanmu kasancewar ba mu san takamammen abinda ya Kai ka ba.
Idon kana son cigaban jihar nan ya zama wajibi ka koma gyefe kabar wannan sabuwar gwamnati ta yi shirinta Wanda take ganin ya kamata domin kai wannan jihar ga tudunbun tsira.
Nagode
Daga Nura Mai Apple
Comments
Post a Comment