Manufar Almajiri a Kasar Hausa
Abin da ake nufi da ALMAJIRI a kalmar Hausa, sunan ya samo asali ne a kasar Hausa tin lokacin da addinin musulunci ya fara samun karbuwa a kasar Hausa, har iyaye suka fara amincewa da bada 'ya'yansu karantarwa a makarantun Tsangayoyin Malaman da suka shigo da ilimin addinin Muslinci a kasar Hausa.
Wanda sukayi imani a wancan lokacin, suka watsar da Bautar Aljani Giji a kasar Hausa, sai suke daukar kyautar Tufafi da Abinci Suna baiwa Almajirai saboda neman tsira da amincin Allah.
Kafin zuwan karantarwar addinin musulunci karkashin tsarin (tsangaya) a kasar Hausa, Ana Bautar Aljannu ne, wadanda ake kira da suna(Giji) a kalmar Hausa, kusan kowane gida akwai (Giji), kuma kowace zuri'ah suna da (Giji), duk wata Masarautar da suka kafu a wancen lokacin suna da Babban (Giji) wanda duk Shekara al'ummar Garin suke Bauta masa duk Gari, idan ana neman Biyan Bukata ana Rokon (Giji) domin a samu biyan Bukata a lokacin jahiliyya.
Daga cikin masu wayo a kasar Hausa tuni sun fahimci (Al'jani-giji) baya iya biya musu bukatunsu, sai suka fara imani da (Ubangiji) bi ma'ana Allah Madaukakin Sarki, wasu kuma sun bijire, suka fifita al'adar kasar Hausa na bautar (Al'jani-giji)akan cewa su bazasu iya barin addinin kakaninsu ba.
Lokacin da Addinin (Ubangiji) ya fara karfi a kasar Hausa, masu bautar (Ubangiji) sun samu mabiya harma sun fara kafa sansani a wasu yankunan kasar Hausa, sai suka daina jihadin fadakarwa aka chanza salon jihadin zuwa yaki da masu bautar (Al'jani-Giji) . Da irin wannan gwagwarmayar mallaman tsangaya suka ruwaito Addinin Allah a kasar Hausa, amma maimakon gwamnati da dubi tsaftacce tsarin sai take kokarin dakatar da tsarin baki daya a kasar Hausa.
Idon aka hana Bara ina makomar marasa galihu? Sanin dukkanin wanda yake a lardin Arewa ne, Al'adar bara ta samo asali ne tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka a kasar hausa. Sannan tun a lokaci ana kallon bara a matsayin wata hanya wanda mutum yake bi domin samun abinda zai ci da abinda zai sha, domin tsayuwa haikan wajen neman ilimin addinin musulunci, da samuwar tarbiyya.
Wannan ne yasa ake safarar yara kanana gari-wa-gari kasa-wa-kasa, zuwa wajen asalin malaman zaure domin samun ilimi mai mai nagarta. Kasancewar bara ya kasu kashi biyu, akwai bara na yara masu karatun allo sannan akwai bara na manyan masu neman tara dukiya. Tabbas mafi yawa daga cikin mutanen da yau suke fada aji a fannin falsafar addinin musulunci, sun samu cikakken ilimin addini, wanda shine ya musu tsani kuma ya masu gata har zuwa wannan lokaci, kuma har gobe ana alfahari da su.
Tabbas duk wanda anka ce ya rufe shagonsa wanda yake neman na rufa, to tabbas ya na bukatar a bude masa babban shagon da zai samu na tuwo, wannan haka yake ko shakka babu.
Tun kafin zuwa wajen magance matsalar barace-barace a cikin al'umma, wanda yafi kamari a yankin Arewa, akwai babbar matsalar da ya kamata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fara fuskanta domin magance ta, shine ilimin neman abun duniya wato; Ilimin Boko, wanda tun lokacin da anka baiwa Najeriya 'yancin kanta, har yanzu abun yaki daidaita.
Idon mukayi la'akari da irin makarantun Boko ko wadanda suke a cikin birane suna fuskantar babban kalubale, balle wadanda suke a cikin karkara. kama tun daga, littatafan Karatu, dakunan gwaje-gwaje, hadi da rashin isasun Uniform na dalibai da harkar ciyarwa, da daidaita albashin malamai, hadi da tantance malamai masu koyarwa a makarantu daban-daban na kowane bangare, idan ilimin boko ya daidaita sannan a dubi yunkurin kawar da barece-barace a cikin al'umma.
Ilimin addini cilas ne ga kowane musulmi, domin yasan yadda zai bautawa Mahaliccinsa, don ya samu tsira a gobe Kiyama, sannan ko ba kada ko sisin kwabo, dole ne Uba ya kawo dansa a makaranta domin neman ilimin addini.
Idan mukayi dogon nazari akan mafi yawa daga almajirai, wadanda sunka sha wahalar makaranta kuma sun ka sha gwaggwarmayar neman ilimi, mafi yawansu yanzu sun koma manyan mutune, sun kama wata sana'ar ta daban suna ci da kansu da iyalansu da 'yan uwansu da abokan arziki. Kasancewar samun ilimin nan da sun kayi tun da farko.
Babban nauyin da rataya ga wuyan gwamnati da shuwagabannin Arewa, idan har zasu yi yunkurin kawar da bara na almajirai to lallai ko sai sun samar masu da hanyoyin dogaro da kai wanda zasu tsayu da kafafunsu wajen neman halalinsu, wadanda sunka hada da; koya musu sana'o'in hannu, kamar Yankan Kunba, shumeka, sayar da tazbi, hadi da sarrafa ta, sayar da turaruka, da sauransu, wanda ta hakan zasu jefi tsuntsu biyu da dutsi daya. Inko ba haka ba, to lallai akwai wata a kasa.
Muna fatan gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagoranci shugaba Muhammadu Buhari, da gwamnatocin Arewa za suyi karatun ta natsu, suyi dogon nazari da hangen nesa, wajen aiki da hikima da dabaru irin na mulki wajen magance abinda ake gani matsala.
Babu wata al'umma da bata son ci gaba, saboda haka muna addu'a da fatan alheri ga kasarmu Najeriya da lardin Arewa. Muna addu'ar Allah yayiwa malummanmu albarka da sunka rikawa iyayenmu ba mu cikakkiyar tarbiyya. Allah ya saka musu da mafificin alheri.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau. 08133376020
Comments
Post a Comment