YA KAMATA JAM'IYYUN ADAWA A JIHAR ZAMFARA SU ƘAURACEWA BABBAN ZAƁEN GWAMNONI DA NA 'YAN MAJALISUN JIHA DAKE TAFE
Ko shakka babu; kamar yadda ta bayyana ƙarara a zaɓen da ya gudana na shugaban Ƙasa da na 'yan Majalisun tarayya a ranar 23 ga fabrairun makon da ya gabata, irin yadda anka samu tarin matsaloli wajen yin zaɓen, Jam'iyyar APC mai ƙarfin fada a ji a cikin jihar ta Zamfara ita tayi uwa, tayi makarɓiya a cikin zaɓen, ma'ana dai ina nufin jam'iyyar tayi amfani da karfin ikon da take da shi, wajen cin karanta ba babbaka a dukkanin inda aka gabatar da zaɓen duk da kasancewar ita shugabar zaɓe ta jihar Zamfara ta tabbatar da za'ayi zaɓe mai cike da sahihanci da tsafta wanda kowa zaiyi na'am da shi. A daidai lokacin da aka wayi garin safiyar zuwa runfunan zaɓe wato ranar Asabar, an samu wasu matsaloli, ta fuskar jinkirin kai kayan zaɓe da wuri, inda wasu rahotannin da muka samu daga wasu jihohin ƙasar nan daban-daban sun dade da fara jefa kuri'unsu, alhali kuma a nan jihar Zamfara ba'a kai kayan zabe ba, duk da tabbacin da hukumar shirya zabe ta ƙasa ta b...