ZUWA GA MABARATAN ZAMANI A SOCIAL MEDIA WAƊANDA SUKA KOMA KARNUKAN 'YAN SIYASA!



Daga Nura Muhammad Mai Apple, Gusau.

Yaɗa ƙarya don samun abin sakawa a baki, babban haɗari ne ga masu aikata hakan da manufar samun na cefane! Labarun bugu wanda ake kira da sunan labarun ƙanzon kurege suna matuƙar cin kare su babu babbaka a cikin wannan zamani da muke ciki.

Duk abinda zakayi sai kayi abisa manufa guda biyu !

1 farko shine; shin abinda kake ƙokarin aikatawa bai ci karo da addininka ba? shin idon har ka aikatashi ba zai jawo maka hushin Ubangiji ba? Idon har ka aikata abin zai amfani wani abu daga cikin addininka ko dai yaya?

2 menene dokokin ƙasa sunka yarje maka ka aikata wanda kuma dokokin sunka baka dukkanin kowace irin cikakkiyar dama. Idon aka samu waɗannan guda biyu a lokaci daya, to zai kyautu ka tsaya waje daya kayi dogon nazari da tunane domin dora kowane daya daga cikinsu abisa ma'aunin hankali sai ka banbance tsakanin aya da tsakuwa.

Sanin kowane musulmi ne da cewa karya tana daya daga cikin abinda Allah Ta'ala yayi hani da ita kuma haramun ce. To micece ribarka idon har kayi karya don kawai abin duniya?

Akwai hanyoyin nema suna da matukar yawan gaske, kuma kowace akwai albarkar da Allah yayi mata.  meyasa ka kasa daukar daya daga ciki kayi amfani da ita domin neman halalinka, ka zabi yin karya don neman  na kalaci?


Ina matukar jin takaici a duk lokacin da naga matasanmu suna yaɗa karyayyaki a kafofin sadarwa domin kwaɗayin abin duniya wanda bashi da tabbas!

Meyasa baku yin duk mai yiwuwa wajen bazama a kafofin na sadarwa kuna kiran gwamnati ta nemo hanyoyin samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa, domin samar da ingantaccen tsaro wanda ta sanadiyar haka ne zamu samu bunƙasuwar arzikin kasa?

Ya Allah ka ganar da matasa mu su gane gaskiya kuma suyi aiki da ita, don mu gudu tare nu tsira tare.



Copyright Mai Apple Gusau

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’