RASHIN GUDANAR DA ZAƁE MAFI YAWA DAGA CIKIN MUTANE SUN TAFKA BABBAR ASARA!



Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau

Hukuncin da hukumar Zaɓe ta ƙasa mai cin gashin kanta da ɗauka na ɗage babban zaɓen da ake sa ran gudanarsa a yau wani babban ƙalubale ne, sannan babu wani gamsashen madogara ko hujja wanda hukumar zatayi godogo da ita, wanda zaisa har mafi yawa daga cikin mutanen Najeriya karɓar uzuri daga wajen Hukumar Zaɓen.


Haka wannan zai zubar da ƙimar Najeriya ga ƙasashen Duniya masu saka ido a zaben na Najeriya, kasancewar za'ayi dubin kamar akwai lauje cikin naɗi akan ɗage zaɓen, an shirya hakan ne kawai domin wata manufa ta tabka maguɗin zaɓe.

Ɗinbin maƙudan kuɗaɗen da jama'a suka salwantar domin shirin zaɓen sun tashi a banza, haka mafi yawa daga cikin al'umma sun baro wasu sassan jihohin da suke neman na sakawa a bakin salati, sun dawo garuruwansu na asali don yin zaɓen, wanda yanzu haka suke cikin nuna damuwarsu a kan wannan ɗage zaɓen.

Wannan dai ya sanya zazzafar muhawara da tsokaci ga masharhanta akan al'amurran yau da kullum a sassan Najeriya dama ƙasashe ƙetare a fannin siyasa dama Demoƙradayyar Najeriya.

Yanzu sau ukku kenan ana ɗaga babban zaɓen na Najeriya, an dai daga zaɓen a shekara ta 2011 da 2015 da kuma 2019, to sai dai wannan karon abun yafi ciwa mutane tuwo a kwarya, kasancewar dubban mutane sun kwanta bacci ne da niyyar yau su halarci runfunan zaɓen, saidai sun wayi gari da jin an ɗage zaɓen, duk da kalaman hukumar na cewa ta shiryawa zaɓen tun gabanin fara shi a yau, amma abin ya canza salo.

Shugaba Bahari na Najeriya mai mulkin ƙasar a yanzu, kuma mai fafutikar ganin ya ɗare kujerar mulkin a karo na biyu, girmansa da ƙimarsa zai zube ga ƙasashe  duniya, duk da ana masa kallon mutum mai gaskiya.


Da wannan muke kira da babbar murya ga hukumar shirya Zaɓe ta ƙasa da cewa tayi duk mai yiwuwa domin ganin hakan bai sake faruwa ba a nan gaba. Fatan alheri da samun ɗorewar tabbatar da mulkin Demokradiyya a Najeriya.

Daga Nura Mai Apple

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’