Skip to main content

Posts

UNITED YOUTH MOVEMENT ASSOCIATION OF ZAMFARA STATE!

Wannan ƙungiyar mai suna a sama! ƙungiya ce wadda anka assasa da zimmar kawo kyakkyawan sauyi mai ma'ana a cikin al'umma, musamman matasa waɗanda sune ƙashin bayan ci gaban kowace al'umma a Duniya. Babu wata ƙasa ko wata al'umma da zata ci gaba matukar ba'a gwama matasa a cikinta ba, kasancewar duk wani babban mutum daga yaro zuwa matashi ya fara. Da sannu wannan ƙungiyar zatayi aiki tuƙuru wajen samar da sauyi mai alfanu a cikin al'ummarta wanda kuma insha Allahu za'ayi na'am da shi. A jiya Asabar 01/12/2018 ne, da misalin ƙarfe 12:01 na rana. Ƙungiyar tayi zamanta na farko a wajen tsohon masallacin Rabi'a dake nan Gusau Babban Birnin Jihar Zamfarar Tarayyar Najeriya. A zaman ƙungiyar na farko ta tattauna akan abubuwa maban-banta daga ciki harda ya za'ayi kungiyar ta kai ga sauran ƙananan Hukumomin da muke da su 14 a cikin wannan jihar ta Zamfara, domin ta samu damar yin aikinta gadan-gadan ba tare da samun wata matsala da kan iya bijirowa ...

TAYA MURNA

Muna amfani da Wannan dama wajen taya murna ga (Amb. Comrd. Nura Isah Gusau) Gwamnan labour Room a Zamfara. Wanda masarautar Gusau ta tabbatar masa da sarautar (DAN-BAIWAN GUSAU) Bisa jajircewarsa wajen yiwa al'umma hidima ba tare da gajiyawa ba. Shakka babu, ka cancanci Wannan sarautar. Muna jinjina ga masarautar Gusau a bisa Wannan karamci da fatan Allah ya taya riko. #Allah_ya_taimaki_Jihar_Zamfara! #Allah_ya_taimaki_Masarautar_Gusau!! #Allah_ya_taimaki_Dan_Baiwan_Gusau!!!

LABOUR ROOM GLOBAL INITIATIVES .... PRESS RELEASE ...

Good day Ladies and Gentlemen of the media.                       In the past few days, we were surprised to learn that few among our Foundation members posted online their official statement of resignation from Labour room cabinet. Despite mixed feelings, Let us start by stating the following: 1. We hereby acknowledge your  contributions to the dynamics of the Labour room. Though, letters were served to each and every appointment/portfolio. Its expected that you write to Labour room Leadership about your intentions rather than addressing it to the general public, but nonetheless, its all for good. 2. The leadership of the labour room global initiatives remain focused, as all those that resigned constitute less than 3% of the entire cabinet. 3. We remain committed to d service to humanity 4. Those outsiders that are not acquainted with the processes of the labour room and genesis of the matter should always endeav...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

NotTooYoungToRun--- Kungiyar Matasa masu Fafutikar Ganin Andama Da Matasa A Harkar Siyasa!

Kasancewar Matasa Sune kashin Bayan ci gaban kowace Al'umma a Duniya, hakan yasa wani bangare daga cikin Matasan Sunka himmatu domin ganin Andama Da Matasa a harkan Siyasa. Matasan Jihar Zamfara, Suma sunbi sauran ayarin Takwarorinsu,  na sassan Kasar nan Da Zimmar gangamin ganin Anrage Tsadar Ticket na 'yan ta karkari domin Matashi Ya samu, halin shiga Shima Adama Da Shi a cikin Harkar Siyasa. Hakika jihar Zamfara, itama Allah Ya hore mata hazikan Matasa masu burin ganin Zamfara ta farfado a cikin Doguwar sumar Da dake Ciki,  Na rashin samun kyakkyawan Shugabanci.  Da wannan muke Kira  da Roko ga Gwamnatin jihar Zamfara, da ta Dubi wannan yunkuri na Matasa, domin Bamu Damar shigowa mu Matasa a harkan Siyasa Don Ci gaban jihar Zamfara da Kasa Baki daya. Rahoto Daga Mai Apple Gusau 

Arewa Youth Mobilization Initiative Nigeria ​AYMi NiG​

  Takardar daga taron bauchi         Assalamu alaikum...    Wannan kungiya mai suna a sama na sanadar dukkanin daukacin ya'yanta musaman masu shirin halartar National Congress wanda kungiyar tayi niyyar gabatarwa a garin a ranar asabar 7/July/2018...   Daga taron ya taso ne bisaga wani tseko na shire shire da ba'akara sa ba...   Daga taron ba yana nufin fasa taron ba ...    Za'agatar da taron a ranakun 27 da 28 a cikin wannan watan na July insha Allahu...     Zamu bukaci jihar bauchi ta kara shire shiren ta akan wanda tayi daga yau zuwa 14 ga watan July domin sanar da al umma domin sauran mahalarta taron su cigaba da shiri tare da samun natsuwa da gamsuwa mai kyau ( Program of events ) na dukkanin ranakun...     Uwar kungiya ta kasa tana bayar da hakuri na daga taron wanda hakan bazaiyi ma wasu dadi ba wannan kada yasa suyi kasa a gwiwa akan tafiyar zata kasance a ranar da aka sata... Sanarwa...........

SHEKARU UKKU CIF-CIF DA DAWOWAR MULKIN NAJERIYA A HANNUN JAM'IYYAR APC MAI ALAMAR TSINTSIYA!

Daga; Nura Muhammad Mai Apple, Gusau Jam'iyyar Apc Mai Alamar tsintsiya Tasamu 'dare madafun Ikon Najeriya a Shekaru Ukku da sunka gabata, wani yunkuri na son Kawo sauyi Mai ma'ana ga Al'ummar Kasa. Jam'iyyun Siyasa Ukku ne sunkayi hadin gwiwa wajan hambarar da mulkin PDP Jam'iyyun dai sune ANPP CPC ACN Wanda a Nata ganin Jam'iyyar Apc  Tana kallon munkin PDP Mai Cike Da Zalunci da Danniya. Inda APC Ta lashi takobin Kwace mulkin a hannun Jam'iyyar PDP Mai Alamar Lema, kuma a karshe wannan yunkuri ya samu gagarumar Nasara. Shin Yaya kuke Kallon Kamun Ludayin Jam'iyyar  APC Shekaru Ukku zuwa yau? Shin Ko kwalliya Ta Fara biyan kudin Sabulu Kuwa? Wane Ci gaba zamu iya cewa Mulkin APC ya Samar? Kuma Wane koma baya za'a iya cewa Ansamu a cikin mulkin Jam'iyyar APC kawowa yau, matakin Kasa Dama Jihohi?