UNITED YOUTH MOVEMENT ASSOCIATION OF ZAMFARA STATE!



Wannan ƙungiyar mai suna a sama! ƙungiya ce wadda anka assasa da zimmar kawo kyakkyawan sauyi mai ma'ana a cikin al'umma, musamman matasa waɗanda sune ƙashin bayan ci gaban kowace al'umma a Duniya. Babu wata ƙasa ko wata al'umma da zata ci gaba matukar ba'a gwama matasa a cikinta ba, kasancewar duk wani babban mutum daga yaro zuwa matashi ya fara. Da sannu wannan ƙungiyar zatayi aiki tuƙuru wajen samar da sauyi mai alfanu a cikin al'ummarta wanda kuma insha Allahu za'ayi na'am da shi.


A jiya Asabar 01/12/2018 ne, da misalin ƙarfe 12:01 na rana. Ƙungiyar tayi zamanta na farko a wajen tsohon masallacin Rabi'a dake nan Gusau Babban Birnin Jihar Zamfarar Tarayyar Najeriya. A zaman ƙungiyar na farko ta tattauna akan abubuwa maban-banta daga ciki harda ya za'ayi kungiyar ta kai ga sauran ƙananan Hukumomin da muke da su 14 a cikin wannan jihar ta Zamfara, domin ta samu damar yin aikinta gadan-gadan ba tare da samun wata matsala da kan iya bijirowa daga baya ba.


Kungiyar matasa ce zallah! masu ƙokarin samar da sauyi. Kuma ƙungiya ce mai zaman kanta, babu wata ƙungiya da tayi hadaka da ita, domin yin aiki tare, 'wannan kenan' sannan kungiyar tana matukar neman goyon bayan al'umma a sassan da muke dasu daban-daban domin samun gamsasun shawarwari, domin ci gaban tafiyar!

KAƊAN DAGA CIKIN AYYUKAN KUNGIYAR SUNE;

Samar da zaman lafiya a cikin al'ummar jihar Zamfara.

Magance shaye-shayen miyagun kwayoyi a cikin matasa, haɗi da hana tu'ammali da su.

Kashe zaman banza a cikin matasa haɗi da samar masu da ayyukan yi.

Hana matasa ta'addanci a lokacin siyasa.

Koyar da matasa sana'o'in hannu, haɗi da basu tallafi domin yin sana'ar.

Taimakon matasa masu karatu, a manyan makarantun da muke da su a cikin jiha da kewaye.

Taimakon matasan da bashi ya kaisu a Gidan kaso wato (gidan yari).

Kaɗan kenan daga cikin ayyukan da kungiyar take ƙudurin yi, a yankunan da muke da su duk a faɗin jiha kwata!



Rahoto Daga; Nura Muhammad Mai Apple Gusau, Publicity U-Y-M-A Zamfara State 08133376020

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’