Yazeed Trust Fund
Operation Taimakon Marayu. Jiya laraba 29/07/2020 gidauniyar Yazeed Trust Fund ta kaddamar da rabon tallafin kayan sallah wa marayu. Wannan aikin alherin da aka saba, ya gudana ne a babban ofishin kungiyar da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara. A lokacin rabon tallafin na kayan sallah, a cikin nasa bawabin shugaban gidauniyar ta Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala UB Gusau ya ce, sun yi wannan nazarin ne la'akari da muhimmancin haka, kasancewar marayu basu da wani galihu, ya kamata su ma a in ganta rayuwarsu a ranar sallah su fito kamar kowa. Taimakon marayu da marasa galihu a cikin al'umma abu ne da ba sabon ba, domin aikin ne wanda ya kasance kamar jini a cikin jikin (Alh Yazeed Shehu Danfulani mai Doya, Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe) bayar da wannan tallafin ya samu halartar manyan mutane da dama daga cikin har da iyaye mata, da sauran al'umma, wadanda suka shedi wannan aikin alheri. Haka shugaban kwamitin bayar da wannan t...