KUNGIYAR YAZEED NETWORK TA KARBI KUNGIYOYIN MATA 7
wasu daga cikin kungiyoyin mata ceo founder Yazeed Network Yazeed Network kungiya ce da aka assasa kuma aka bude ta domin tafiya kafada-da-kafada da sauran kungiyoyin dake fafutikar ilmantar da al'umma, hadi da wayar da kan al'umma akan manufofi hadi da bayyana alherai na (Alh Yazeed Shehu Danfulani Mai Doya), wadanda yake yi ga al'umma. Wata jigo daga cikin babbar kungiyar Yazeed Trust Fund ce ta kirkiri kungiyar, domin hada karfi da karfe, wajan wannan gwagwarmaya. Hajiya Aliya Saraki, ita ce shugabar Kungiyar Yazeed Network. A kokarin kungiyar na ganin ta zakulo kungiyoyin mata a sassa daban-daban na jihar Zamfara, a Ranar alhamis din da ta gabata ta karbi wasu gungun kungiyoyin mata 7 wadanda suka jaddada goyon bayansu ga tafiyar (Alh Yazeed Shehu Danfulani Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe). Jawabin shugabar kungiyar a yayin taron ta jinjina wa tawagar wadannan kungiyoyi tare da shan alwas...