WANE TSARI GWAMNATIN TARAYYA DA NA JIHOHI SUN KA YIWA MASU DAN KARAMIN KARFI, BAYAN SANYAWA KASA DA JIHOHI TA KUNKUMI, DON BAYAR DA KARIYA GA CUTAR KORONA?
Duk da kasancewar cutar Karona cuta ce mai matukar hatsarin gaske, tun daga saurin yaduwa kamar wutar daji, ga kuma saurin kisa, idan mu kayi tsinkaye ga dubban al'ummar da wannan cuta ta hallaka a yankuna daban-daban na duniya, wanda hakan ya sa hatta a kasashen duniya masu karfin fada aji, da kuma karfin tattalin arziki sun girgiza sosai a sanadiyar wannan cuta. Iya binciken masani fannin lafiya da kuma bincike mai zurfi sun tabbatar da har kawowa wannan lokaci babu ainihin takamammen maganin wannan cuta mai toshe lunfashi. Wanda haka yasa kasashen duniya suke ci gaba da garkame kan iyakokinsu, domin takaita illar cutar. Kasashe daban-daban na duniya suna fitar da wani tallafi na musamman domin bayarwa ga ilahirin al'ummarsu, wanda hakan zai rage masu radadin halin matsi da suke ciki, sakamakon killacesu da akayi a gida, har zuwa lokacin da gwamnatocin kasashen sun ka kaiyade fara zarga-zarga. Tuni ita ma Najeriya na shiga cikin jerin gwanon gwamnatocin duniya wa...