Zuwa ga mai girma Gwamnan Jihar Zamfara
Assalamu alaikum. Bayan sallama irin ta addinin musulunci, cike da girmama a matsayina na talakanka, kuma wanda yake a karkashin jagorancinka a wannan jiha tamu mai albarka wanda bamu da wata jiha bayanta. Nake bayyana ra'ayi na, a bisa wannan nazari naka na ganin jihar Zamfara ta kece tsara a sauran jihohin da muke da su a cikin kasar nan na gina sabon gidan gwamnati la'akari da irin yadda aka barmu a baya ta gefen babban gida, mallakar gwamnati. Babu ko shakka wannan nazari ne mai kyau kuma abun so ne, kuma ci gaba ne mai alfanu, Allah ta'ala ya mana jagora, Amin! Ba zan so na kaucewa daftarin tsarin dokar kasar nan ba, na damar da aka bawa 'yan kasa na fadin albarkacin baki, cikin sashe na 39 karamin sashe na kundin tsarin mulkin kasar nan. A kowane lokaci irinmu masu nazari da sharhi akan al'amurran yau da kullum ba'a rasa mu da tsegumi akan wasu abubuwa mabambanta akan abunda suka shafi kasar nan dama wasu jihohi wani lokacin ma har da wasu kasashen...