A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!
A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...