An kai harin bam a kasuwar garin Mubi dake jihar Adawama a arewa maso gabashin Najeriya.



Abin fashewa na farkon dai ya tashi ne a kusa da wani masallaci da ke layin ‘yan gwanjo a kasuwa garin da misalin karfe sha biyu da rabi.

Jim kadan kuma sai daya abin fashewar ya tashi a kusa da inda na farkon ya tashi.

Wani wanda ya shaida lamarin ya ce yayin da mutane suke tserewa daga kasuwar, sun ga jami’an tsaro suna tafiya wurin.

Ya kara da cewa an yi ta kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su a cikin keke Napep.

Sai dai kuma kawo yanzu babu tabbatcin iya wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata a harin.

Babu wata kungiyar da ta dau alhakin kai wannan harin, amma kungiyar Boko Haram takan kai hare-haren kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’