Zuwa Ga Mai Daraja Gwamnan Jihar Zamfara a Kan Makomar Jihar
Zamfara jihace wadda a cikin kasar nan idon akayi magana a kan zaman lafiya ita ce kan gaba kafin wasu jihohi, shekaru 20 da suka gaba ta, duk wani dan jihar Zamfara idon zai kwanta bacci baya rufe gidansa. Mafi yawa daga cikin gidajen al'umma a wancen lokaci bud'e suke kwana har safe, saboda zaman lafiya. A wancen lokacin komai dare mutum baya jin tsoron tashi daga wannan gari zuwa wancen, daga wannan unguwa zuwa waccen, domin baya tsaron komai. A wancen lokacin dabbobi suna kwana a cikin daji, alhali mai su yana cikin gari hankalinsa akwance a natse! Baya tsoro wani abu. Dukkan kasuwannin dake fadin jihar suna gudana cikin dadin rai, duk da ana kallon a wancen lokacin kamar arziki bai yilwatu ba a cikin al'umma, amma zaman lafiya ya samu, kwanciyar hankali a ko'ina. Al'umma suna gudanar da rayuwarsu irin yadda suke so, babu tsamgwama, babu hantara, ko kyara! Kaiconmu! Duk wanda ya rayu a wancen lokacin, kuma yana raye a yanzu, ya ga abin mamaki da fa...