KYAUTAR GIRMAMAWA DAGA YAZEED TRUST FUND ZUWA GA JEKADIYYAR YAZEED
Shimfiɗa. Lambar yabo ta girmamawa wanda ake kira da (award) a turance wata babbar kyauta ce wadda ake bayarwa ga dukkan wanda ya shahara ta wasu fuskoki, misali; wanda ya kasance ɗan gwagwarmayar rayuwa a gefen da ya fi shahara haɗi da kwarewa, domin ƙara masa kwarin gwiwar tashi tsaye domin kara azama akan abinda yasa a gaba, domin ganin nasararsa ta ci gaba da ɗorewa har iyakar rayuwarsa. Madallah da lambar yabo ta girmamawa ga wanda ya cancanta! A 19/08/2020 gidauniyar nan mai yaɗa manufofi haɗi da yin ayyukan alheri a cikin al'umma a duk faɗin jihar Zamfara, kuma mai son ganin al'umma sun samu kowane irin sauye-sauye ta fuskar samarwa da jama'a ingantacciyyar rayuwa, wadda ke ƙarƙashin kulawar (Alh Yazeed Shehu Dan Fulani) wanda (Comrade Rufa'i Bala UB Gusau) yake shugabanta wato; (Yazeed Trust Fund) ta karrama daya daga cikin jiga-jigan gidauniyar, wato; (Hajiya Aisheet Ibraheem, mai laƙabi da 'yar Asali'. An dubi yiwuwar, haɗi da nazarin bata wannan kyau...