KALAMAN GWAMNA BELLO MUHAMMAD MATAWALLE NA JIHAR ZAMFARA A KAN TSOHON GWAMNA AA YARI
a falsafa irin ta siyasa wanda muke gani tana gudana a daidai wannan lokaci, bayyane take karara kalaman gwamnan jihar Zamfara (Rt,Hon Bello Muhammad Matawallen Maradun) jan kunne ne ga tsohon gwamnan jihar Zamfara (Dr, Hon Abdul-aziz Abubakar Yari shattiman Zamfara) kuma jan kunne ne ga dukkanin wani mai kokarin yin tugu ga zaman lafiyar da ake ganin jihar ta samu tun bayan kame madafun ikon da shi wannan gwamna Bello Matawalle yayi. Idan muka yi dubi a mahanga irin ta siyasa zamu ga cewa mutum zai iya yin duk wani abu domin cimma wata manufa ko da kuwa hakan zai iya bakanta ran dubban al'umma, faifan bidiyon da ya bayyana a ranar Alhamis 21 ga watan Satumbar 2019 ya ja hankulan dubban mutane a sassa daban-daban na kasar nan da wasu kasashen ketare, inda an ka gano gwamnan Bello Matawalle shi da kansa ya na bayyana irin ƙwaƙwaran matakin da zai dauka ga tsohon gwamnan AA Yari. Idan dai zamu iya tunawa gwamnan ya sha kiran taron 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC a gid...