Skip to main content

GWAMANATIN JAHAR ZAMFARA ZA TA DAUKI NAUYIN DALIBBAI SU YI KARATUN LIKITANCI A JAMI'AN NAJERIYA DA KASASHEN WAJE



Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara, Hon. Dr. Bello Mohammed, Matawallen-Maradun ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dauki 'yan assalin jahar Domin su yi karatun likitanci da sauran kwasa-kwassan kiyon lafiya a jami'o'in kasarmu Najeriya da na kasashen waje.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin 'ya'yan kungiyar likitoci Reshen jahar Zamfara  wato Nigeria Medical Association (NMA) a turance, da su ka kawo masa ziyarar taya murna a fadar Gwamnatin jahar Zamfara da ke Gusau.

Gwamnan ya bayyana cewa yana daga cikin gudurinsa, na farfado da sha'anin kiyon lafiya da ya yi matukar gurgurcewa, Dan haka gwamnatinsa take zimmar daukar nauyin karatun  'yan assalin jahar Zamfara Domin karatun bangaren likitanci da sauran kwasa-kwassan kiyon lafiya .

In dai ba a manta ba Tun a ranar karbar ranstuwar gwamnan ya yi alkawarin cewa Mata Da kananan yara za su mori kula da lafiyarsu kyauta. Sai dai haka ba zai samu ba sai an samu wadatattu jami'an kiyon lafiya da kayan aiki isassu.

Dan gane da neman da 'ya'yan kungiyar su ka yi na Gwamnatin jahar Zamfara ta aiwatar da shirin nan na CONMESS Da zai gyara albashin likitocin Da ke aiki jahar Zamfara. Gwamnan ya yi alkawarin zai dubi llamarin.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi aiki kafada-da-kafada da 'yan kungiyar. Domin habbaka sha'anin kiyon lafiya na jahar Zamfara, zuwa matakin kasa-da-kasa ta yadda al"ummar Zamfara za su amfana.

Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa tuni dai ya umurci ma'aikatar kiyon lafiya, da ta turo masa Da bayanan assibitocin jahar Zamfara da abunda assibitocin su ke bukata Domin dacewa da Zamani. Da kuma kayan da ke kasa a cikin assibitocin.

Tun da farko shugaban kungiyar na jahar Zamfara, Dr. Kabiru Musa ya bayyana cewa sun zo a fadar Gwamnatin ne, Domin domin taya gwamnan murna akan nasarar da ya samu na zama gwamnan jahar Zamfara, Dan haka ya roki Allah ya rikawa gwamnan ya Sanya albarka a jagorancinsa.

Shugaban kungiyar, ya yi amfani da wannan damar inda ya jawo hankalin gwamnan jahar Zamfara. Akan mawuyacin halin da membobinsa ma'aikatan kiyon lafiya su ke ciki, idan aka daidaita su da takwarorinsu da ke a makwabtan jahohi, ta fuskar albashi, da rashin kayan aiki a dukannin Manyan assibitocin jahar dama kananan assibitocin, Wanda haka ya taimaka matuka gaya ga rashe-rashen da ake samu na musamman ga Mata masu haihuwa. Wanda ya baiwa gwamnan bayanan wadannan matsalolin a rrubue.

 Yusuf Idris GUSAU

Babban Daraktan Watsa Labarai Labarai A Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara

Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

06/07/2019

Comments

  1. Allah yataimaki gwamnatin jahar zamfara yakuma bata nasarar cika wadannan kyawawan manufofi nata ameen

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!

A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...