Skip to main content

WASU DAGA CIKIN 'YA'YAN KUNGIYAR KWADAGO A JIHAR ZAMFARA SUN TADA JIJIYOYIN WUYA AKAN RABON ABINCI!






Wasu mutane idon har aka zo wajen fannin abinci, sunfi kowa wuyar lamari, shidai abinci abu ne wanda akeyi domin ci a daina jin yunwa, kuma abinci yana da ka'idadden lokaci wanda idon har lokacin ya wuce  ba'ayi amfani da shi ba, zai iya lalacewa, musamman abinda ya shafi dafaffar Shinkafa haka tuwo kowane iri ne, haka Alala ko danwake da dai sauran dangogin irin abincinmu na gargajiya.

Wani abun mamaki da ban haushi da takaici wanda ya faru a yau wajen gagarumin taron kungiyar kwadago, wanda ake gabatarwa duk shekara-shekara, a al'ada ansaba karrama dukkanin wanda aka bashi goron gayyata kuma ya karba gayyatar ya samu halartar wajen da abinci da abin sha, domin rage gajiyar da aka kwasa wajen rangadin. kuma kungiyar ita take daukar nauyin abinci ga al'umma.

Wasu daga cikin wadanda aka a zawa nauyin rarraba abincin ga al'umma, sun wulakanta mutane yadda ransu yake so, yayinda sunka yi amfani da damar wajen baiwa wanda ransu yake so. Kungiyar muryar talaka ta Kasa Reshen Jihar Zamfara tana daya daga Cikin kungiyoyin da aka baiwa goron gayyata kuma ta samu halartar wurin, sannan wadannan bayin Allah  sun kalli 'ya'yan kungiyar da jajayen idonu! inda karshe dai basu karbi komai daga wajenba.

Muna kira da babbar Muryar ga kwamitin da ake daurawa alhakin wannan bangare da suji tsoron Allah su kyautata aikinsu kasancewar Kungiyoyi ba abin walakantawa bane, musamman Kungiyar Muryar Talaka wanda duk Najeriya ko ina ana alfahari da ita. kasancewarta kungiyar Talakawa zallah, har masu hannu da shuni suna amfana da ita.

Allah ya kyauta!

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020