AN GUDANARDA BUKIN RANAR MA'AIKATA A JAHAR ZAMFARA A YAU
Ma'aikatan Jihar Zamfara suma sunbi Takwarorinsu wurin Gudanar da Bukin Ranar Ma'aikata ta Duniya Kuma Bukin ya Gudana a cikin makarantar Zakas Kamar yadda aka saba duk shekara dake Gusau jihar Zamfara, kuma an gudanarda Bukin Karkashin Jagorancin Shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar Zamfara. Comrd. Bashir Mafara.
Kuma Bukin ya samu halartar Kungiyoyin Kwadago daban-Daban wadanda Sunka hada da NLC, NULGE, TUC, NUJ, NUT, ASCSN, NCSU. SSANU, muryar talaka, Mata basu dubara, Rattawo Da dai sauransu.
Inda taron ya samu wakilcin Maigirma Gwamnan Jihar Zamfara Alh Sanda Ɗan Jari Kwatarkwashi, bikin ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.
Muna fatan itama jihar Zamfara zata bi sahun wasu takwarorinta wajen ƙara zage damtse domin jin ɗaɗin ma'aikatanta.
*Allah ya taimaki Jihar Zamfara, da ma'aikatanta! Allah ya taimaki Najeriya da ma'aikatanta! Allah ya maimaita.*
Daga Nura Mai Apple Gusau ɗan Ƙungiyar Muryar Talaka ta ƙasa Reshen Jihar Zamfara
Copyright@nuramaiapplegusau
Comments
Post a Comment