Posts

Showing posts from May, 2019

WASU DAGA CIKIN 'YA'YAN KUNGIYAR KWADAGO A JIHAR ZAMFARA SUN TADA JIJIYOYIN WUYA AKAN RABON ABINCI!

Image
Wasu mutane idon har aka zo wajen fannin abinci, sunfi kowa wuyar lamari, shidai abinci abu ne wanda akeyi domin ci a daina jin yunwa, kuma abinci yana da ka'idadden lokaci wanda idon har lokacin ya wuce  ba'ayi amfani da shi ba, zai iya lalacewa, musamman abinda ya shafi dafaffar Shinkafa haka tuwo kowane iri ne, haka Alala ko danwake da dai sauran dangogin irin abincinmu na gargajiya. Wani abun mamaki da ban haushi da takaici wanda ya faru a yau wajen gagarumin taron kungiyar kwadago, wanda ake gabatarwa duk shekara-shekara, a al'ada ansaba karrama dukkanin wanda aka bashi goron gayyata kuma ya karba gayyatar ya samu halartar wajen da abinci da abin sha, domin rage gajiyar da aka kwasa wajen rangadin. kuma kungiyar ita take daukar nauyin abinci ga al'umma. Wasu daga cikin wadanda aka a zawa nauyin rarraba abincin ga al'umma, sun wulakanta mutane yadda ransu yake so, yayinda sunka yi amfani da damar wajen baiwa wanda ransu yake so. Kungiyar muryar talaka t...

AN GUDANARDA BUKIN RANAR MA'AIKATA A JAHAR ZAMFARA A YAU

Image
Ma'aikatan Jihar Zamfara suma sunbi Takwarorinsu wurin Gudanar da Bukin Ranar Ma'aikata ta Duniya Kuma Bukin ya Gudana a cikin makarantar Zakas Kamar yadda aka saba duk shekara dake Gusau jihar Zamfara,  kuma an gudanarda Bukin Karkashin Jagorancin Shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar Zamfara. Comrd. Bashir Mafara. Kuma Bukin ya samu halartar Kungiyoyin Kwadago daban-Daban wadanda Sunka hada da NLC,  NULGE, TUC, NUJ,  NUT, ASCSN, NCSU. SSANU,  muryar talaka, Mata basu dubara, Rattawo Da dai sauransu. Inda taron ya samu wakilcin Maigirma Gwamnan Jihar Zamfara  Alh Sanda Ɗan Jari Kwatarkwashi, bikin ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana. Muna fatan itama jihar Zamfara zata bi sahun wasu takwarorinta wajen ƙara zage damtse domin jin ɗaɗin ma'aikatanta. * Allah ya taimaki Jihar Zamfara, da ma'aikatanta! Allah ya taimaki Najeriya da ma'aikatanta! Allah ya maimaita. * Daga Nura Mai Apple Gusau ɗan Ƙungiyar Muryar Talaka ta ...