RA'AYIN MAI APPLE AKAN SIYASAR KANO
Assalamu alaikum, barkarmu da yau barka da wannan lokaci tare da fatan dukan masu bibiya ta a kafofin sadarwa daban-daban suna cikin koshin lafiya, ya a kaji da fama? Yau ra'ayin nawa zai maida hankali ne kachokan akan siyasar wata jiha daga cikin manyan jihohin Najeriya kuma jiha mafi yawan al'umma a Najeriya, wato jihar Margayi malam Aminu Wato Kano kenan. Tabbas jihar kano jiha ce wanda Allah madaukakin sarki ya arzuta ta da mutane masu hazaka da basira da kwazo da sanin ya kamata, sannan kanawa mutane ne, masu kawaici da nuna da'a da dattako. Tun farkon samuwar wannan kasar tamu, wato Najeriya, tun lokacin zamunna daban-daban da suka shude, Jihar kano sananniya ce wajen kokarinta na kawo dukan cigaban da za'ayi alfahari da ita, wanda a cikin jajircewar ta ne yasa Arewa tayi fice kuma ta samu daukaka ƙima da daraja a idon Duniya. Kamar dai yadda masu salon iya zance suke fada da cewa ''Kano Ta Dabo Tunbin Giwa yaro Ko Dame kazo Anfika'' ko shakk...