Matsalar Mai: Kungiyar ‘Yan Jarida A Jahar Barno Ta Zargi Jami'an Mai
Kodayake matsalar mai ta fara lafawa a wasu sassan arewacin Najeriya, ganin yadda matsalar ta dada rikita al’amura a arewa maso gabashin Najeriya, musamman ma jahar Barno, Kungiyar ‘Yan Jarida (NUJ), shiyyar jahar ta daga yatsa ma manyan ma’aikatan bangaren man fetur, wadanda ta zarge da barin wasu masu zalama da haddasa matsalar.
Bayan yankin arewa maso gabashin Najeriya ya sha fama da karancin da kuma tsadar mai, musamman ma wanda aka yi kwanan nan, Kungiyar ‘Yan Jaridar Najeriya Shiyyar jahar ta Barno ta zargi manyan ma’aikatan bangaren main a Najeriya da rashin tabukawa sosai wajen dakile matsalar.
Kungiyar ta yi nuni da yadda Mataimakin Shugaban Najeriya Furfesa Yomi Osunbajo ya yi ta kai koma wajen ganin matsalar ta kau. Kungiyar ta ce sam manyan ma’aikatan bangaren mai bas u taimakawa kuma sun bar wasu manyan ‘yan kasuwa na cin karensu ba babbaka.
Da yake karin haske ma wakilinmu a jahar Barno, Haruna Dauda, Shugaban kungiyar ‘yan jaridar, Shiyyar jahar Barno, Baba Sheikh Haruna y ace ya zama wajibi su fitar da takardar yin Allah wadai da manyan jami’an bangaren mai din saboda yadda su ka bari masu son kazamin ribi na ta gasa ma jama’a aya a hannu. Ga Haruna Dauda da cikakken rahoton:
Comments
Post a Comment