Masar ta yanke wa tsohon shugaban kasa Morsi tare da mutane 19 shekaru uku a gidan kaso bisa laifin zagin hukumar shari’ar kasar
A shekara 2013 shugaban kasar masar na yanzu Abdul fatah El Sisi yayi wa Mohammed Morsi juyin mulki
Wata kotu a Cairo babban birnin kasar Masar ta yankewa tsohon shugaban kasar Masar, Mohamed Morsi, tare da mutane 19 shekaru uku a gidan kaso da biyan diyar $112,700 bisa laifin zagin hukumar shariar kasar.
A cikin sauran mutanen da kotu tayi musu sharia hadda daya daga cikin manyan masu neman yanci dan Adam na kasar masar, Alaa Abdel Fattah, da wani babban ma’aikacin gidan talabijin, Tawfik Okasha.
Masar ta yanke wa tsohon shugaban kasa Morsi tare da mutane 19 shekaru uku a kurkuku don zagin hukumar shari’ar kasar
Amma suna da yanci daukaka kara.
A shekara 2013 shugaban kasar masar na yanzu, Abdel Fattah al-Sisi, ya yiwa Mohammed Morsi juyi mulki bayan yan kasar sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin goyon bayan gwamnatin sa.
Bayan anyi ma sa juyin mulki, kotu ta yanke masa hukunci shekaru 20 a gidan kaso bisa laifin kashe masu zanga-zanga a shekara 2012, da kuma kari shekaru 25 akan laifin taya kasar Qatar lekan asiri.
Comments
Post a Comment