Babban Bankin Duniya ya yabawa Gwamnatin Najeriya na damawa da ‘Yan kasuwa
Mun samu labari mai dadi a karshen shekarar da ta gabata inda aka bayyana cewa Najeriya na cikin kasasshen da su kayi zarra wajen tsarin hulda tsakanin ‘Yan kasuwa da Gwamnati Inji Babban Bankin Duniya.
A jerin da WBG na babban Bankin Duniya ta fitar, Najeriya ce ta 4 a kaf Duniya wajen mu’amala tsakanin ‘Yan kasuwa masu cin gashin kan su da kuma Gwamnatin Kasar. Najeriya tana cikin wadanda su ka taka rawar gani kwarai a bara.
Kungiyar ICRC mai kula da jinginar kadarori da sauran su tayi abin a-yaba a Duniya a shekara nan da ta wuce inda ta zama ta farko a cikin sauran Hukumomin Duniya da ta bude shafi musamman domin fayyace ayyukan ta a yanar gizo.
Shugabar Hukumar ta ICRC Chidi Izuwah cewa tayi aikin da su kayi ya kara ba masu hannun jari kwarin gwiwa game da Gwamnatin Kasar. Tun farkon mulkin sa, Shugaba Buhari ya nemi ‘Yan kasuwa su dafa wajen gina abubuwan more rayuwa.
Comments
Post a Comment