2019: Buhari ya nada Amaechi darektan Kamfen din sa



Rahotanni sun kawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada ministan sufuri, Rotimi Ameachi a matsayin shugaban kamfen din sa a zaben 2019.

Wannan shine karo na biyu da shugaban kasar ke daura shi akan wannan mataki.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Amaechi ya karbi wasikar nada shi daga fadar shugaban kasa kuma zai sanar wa duniya a mako mai zuwa.

A cewar jaridar, bincike da ta gudanar na musamman domin sanin tabbacin wannan rahota ya nuna mata cewa akwai kamshin gaskiya a maganar.

Kaduna yayinda Buhari zai ziyarci jihar
Majiyar tamu ta ce kakakin Amaechi, David Iyofor, ya shaida mata cewa ba zai iya cewa ehhh ba, kuma ba zai ce a’a ba.

Ba tun a yau bane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke nuna alamun cewa zai fito takara a 2019. Ya fadi wani abu mai kama da haka da ya ziyar ci mutanen jihar Kano.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’