Posts

Showing posts from February, 2020

KUNGIYAR STUDENT ALLIANCE SUPPORT OF BELLO MUHAMMAD MATAWALLE (SA-BELMAT)

Image
KUNGIYAR STUDENT tayi zama yau daya daga cikin wadanda suka kirkiro da wannan kungiya wato Comrade Umar Mahmud Umar, ya ce; "babban makasudin zaman shine munga ya dace mu fito a matsayinmu na 'yan jiha, kuma a matsayinmu na wani yanki daga cikin daliban jihar Zamfara muyi godiya ta musamman bisa ga irin gwaggwarmaya da chanji da Hon Luqman Majidadi ya kawo karkashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Zamfara na bashi wannan jagorancin, da kuma shi gwamna a bisa babban aikin da ya dauko wajan ganin a samu ilimi a cikin jihar Zamfara". Ya ce; "kamar yadda muka sani akwai dalibai wajan 700 daga jihar zamfara wadanda aka dauko kuma aka tantance mutum 200 daga ciki zasu je suyi karatun a bangare daban-daban tun daga abinda ya shafi bangare tiyata da kuma hada magunguna da sauransu, wanda insha Allahu nan da shekaru zuwa goma zamu samu 'yan asalin  jihar Zamafar da suka samu kwarewar da zasu ci gaba da kula da 'yan uwansu a cikin kauyuka da kuma biranen jihar...