Posts

Showing posts from December, 2018

UNITED YOUTH MOVEMENT ASSOCIATION OF ZAMFARA STATE!

Image
Wannan ƙungiyar mai suna a sama! ƙungiya ce wadda anka assasa da zimmar kawo kyakkyawan sauyi mai ma'ana a cikin al'umma, musamman matasa waɗanda sune ƙashin bayan ci gaban kowace al'umma a Duniya. Babu wata ƙasa ko wata al'umma da zata ci gaba matukar ba'a gwama matasa a cikinta ba, kasancewar duk wani babban mutum daga yaro zuwa matashi ya fara. Da sannu wannan ƙungiyar zatayi aiki tuƙuru wajen samar da sauyi mai alfanu a cikin al'ummarta wanda kuma insha Allahu za'ayi na'am da shi. A jiya Asabar 01/12/2018 ne, da misalin ƙarfe 12:01 na rana. Ƙungiyar tayi zamanta na farko a wajen tsohon masallacin Rabi'a dake nan Gusau Babban Birnin Jihar Zamfarar Tarayyar Najeriya. A zaman ƙungiyar na farko ta tattauna akan abubuwa maban-banta daga ciki harda ya za'ayi kungiyar ta kai ga sauran ƙananan Hukumomin da muke da su 14 a cikin wannan jihar ta Zamfara, domin ta samu damar yin aikinta gadan-gadan ba tare da samun wata matsala da kan iya bijirowa ...