NotTooYoungToRun--- Kungiyar Matasa masu Fafutikar Ganin Andama Da Matasa A Harkar Siyasa!
Kasancewar Matasa Sune kashin Bayan ci gaban kowace Al'umma a Duniya, hakan yasa wani bangare daga cikin Matasan Sunka himmatu domin ganin Andama Da Matasa a harkan Siyasa. Matasan Jihar Zamfara, Suma sunbi sauran ayarin Takwarorinsu, na sassan Kasar nan Da Zimmar gangamin ganin Anrage Tsadar Ticket na 'yan ta karkari domin Matashi Ya samu, halin shiga Shima Adama Da Shi a cikin Harkar Siyasa. Hakika jihar Zamfara, itama Allah Ya hore mata hazikan Matasa masu burin ganin Zamfara ta farfado a cikin Doguwar sumar Da dake Ciki, Na rashin samun kyakkyawan Shugabanci. Da wannan muke Kira da Roko ga Gwamnatin jihar Zamfara, da ta Dubi wannan yunkuri na Matasa, domin Bamu Damar shigowa mu Matasa a harkan Siyasa Don Ci gaban jihar Zamfara da Kasa Baki daya. Rahoto Daga Mai Apple Gusau